Meye Gaskiyar Kara Makin Jarabawa JAMB Wato JAMB Score Upgrade



Duba dayadda dalibai ke shiga tsaka mai wuya a lokacin da suka fadi jarabawar sharen fage na shiga jami'a wato JAMB, hakan yaba da dama ga wasu gurbatatun mutane  su yaudara dalibai da suna JAMB SCORE UPGRADE domin su danfare su. shafin my arewa school yayi nazari akan batun JAMB SCORE UPGRADE.


MENE NE JAMB SCORE UPGRADE ?


Jamb score upgrade kalmar turanci ne da ke nufin "kara maki a jarabawar JAMB".


Wanda wasu tsirarun mutane yan danfara suke ikirarin sunayi domin danfarar daliban da suka sami maki kadan bayan gudanar da jarabawar ta JAMB.


SHIN YA HALACIN JAMB SCORE UPGRADE YAKE ?


Shi dai JAMB score Upgrade ba halataciyar abu bane kuma ba daga hukumar jarabawar JAMB ya ke ba, haka zalika yasabawa dokokin hukumar jarabawa JAMB.


Hasali ma bai da tushe balantana makama a hukumar jarabawar JAMB.


HANYOYIN DA DALIBI ZAI BI DAN GUJE WA DANFARAR  JAMB SCORE UPGRADE


1. Dalibi ya kamata yasani cewa babu wani jami'in hukumar JAMB da zai iya kara masa maki domin kuwa komai yanzu da computer akeyi, sa'anan a riga anyi programming din jarabawar tunda ga gun rubutawa har da zuwa marking.


2. Dalibi yazama dole ya guje wa masu cewa suna yin upgrade na maki jarabawar domin kuwa yan damfara ne.


3. Dalibi ya kamata yasan cewa babu yada za'ayi hukumar jarabawa tayadda da jamb score upgrade ko ta fito da tsarin upgrade din maki domin daliban da suka fadi.


4. Kada dalibi ya yadda yaba wa kowa wani bayani sa na jarabawar, don ya taimakesa ya kara masa maki.


Inhar dalibi yakiyaye wa inan da wasu kaidoji toh babu wanda zai damfare sa da sunar JAMB Score Upgrade.


Post a Comment (0)
tsoffin labarai Sabbin Labarai