Abubuwan Da Dalibai Ke Bukata Kafin Cika Form Din Post UTME Na Nubapoly



Kamar yada kowa yasani post UTME shine mataki na biyu bayan dalibi ya wuce jarabawar JAMB, don samun gurbin Karatu a makarantar gaba da sekandiri.


Sanan kowace makaranta na da haqqi kan yada zata tsara post UTME din ta wasu ta hanyar tantace wa a yarnar gizo wasu kuma gun rubuta jarabawa.


Nuhu Bamali Polytechnic dake Zaria, ita ma na da tsarin gun rejista post utme ga dalibai dake neman gurbi karatu a makarantar.


ABUBUWAN DA DALIBI KE BUKATA KAFIN YAYI RIJISTAN POST UTME NA NUBAPOLY SUN HADA:


 1.  Dole sai dalibi yana da credits 5 a jarabawar Olevel (WAEC,NECO,NABTEB,NBAIS).

 2. Dole dalibi sai yasa makaratar NUBAPOLY a matsayin zabin sa na farko  a jarabawar JAMB.

 3. Dole dalibi sai yaci adadin maki da hukumar jarabawar JAMB da masu ruwa da tsaki suka amince a matsayin adadin maki bada gurbi karatu a polytechnic dake Nijeria.

 4. Dalibi ya kasance yana da sahihin adreshin Email .

 5. Dalibi yatabatar yanada number waya.


Wanan na daga cikin ababen da dalibi ke bukata kafin cika Post UTME form na makarantar Nuhu Bamali Polytechnic dake Zaria.

Post a Comment (0)
tsoffin labarai Sabbin Labarai