(ASUU-UMYU) Ta Shawar Ci Dalibai Su Cigaba Da Zama A Gida




Bayan sanarwa da jami'ar Umaru Musa Yar'adua tayi kan batun bude makaranta aranar 19 ga watan oktoba 2020.


kwatsam sai kungiyar ASUU rashen makarantar sukace bude makaranta bai shafi tsarin kungiyar ba hasalima alhakin hukumar makaranta ne ta sanar da ranar bude wa.


Adalilin cigaba da fafatukan cinma matsaya tsakanin uwar kungiyar da gwamnati, Kugiyar sunce ba za su lamunci kowane malami ya koyar da dalibai ko ya duba aikin project na dalibai ko kuma wani tataunawa ba da sauransu.


Inda akarshe suka shawarci dukan  daliban jami'ar  cewa kada su dawo makaranta har na tsawon mako guda har sai uwar kingiyar ta Nijeria ta cimma matsaya da gwamnatin taraya.


Post a Comment (0)
tsoffin labarai Sabbin Labarai