A wani toron da hukumar makarantar Hassan Usman Polytecnic Katsina, na musamman da ya guda na a ranar 14 ga watan Octoba 2020, hukumar makarantar ta tattauna batutuwa aciki harma da ranar da za a bude makarata bayan bular cutar covid-19.
Hukumar ta amince da abubuwa kamar haka:
1. Hukumar ta amince a bude makarantar a ranar 26 ga watan oktoba 2020, don karasa zango karatu na farko a kakar shekarar 2019/2020.
2. Hukumar ta amince da wa'adin sati 3 domin bita karatu ga dalibai kafin fara jarabawar zango farko.
3. Hukumar ta amince da cigaba da karatun zango na biyu bayan kamala jarabawar zangon farko.
Hukumar ta jan kune dukan dalibai da malamai gurin bin dokokin kare kai da cutar corona, ta hanyar amfani da facemask da bada tazara a dakunan kwana da ajujuwa karatu tare da wanke hanu akai akai da sinadarin hand sanitizer.