An sauya Ranar Rubata Jarabawar NECO Sabida Musu Zanga Zangar #ENDSARS

 


Hukumar rubuta jarabawa National Examination Council(NECO), Ta sauya ranar da za'a rubuta jarabawar  Computer Studies Practical wadda yakamata a rubuta a ranar 19 ga watan oktoba 2020 zuwa ranar  16 ga watan Nuwamba 2020. Sanar wa yafito ne daga  Azeez Sani, jami'i mai kula da huldar jama'a na hukumar.


Azeez yace sauyin ranar ya biyo bayan  rashin samun hayayi raba takadun jarabawar ne wanda masu zanga zanga #ENDSARS suka janyo  ta hanya cika tutuna.


Duk da kokarin da akayi na tura takardun kwanaki biyu kafin jarabawar ama hakan bai cima ruwa ba, adon haka aka yanke shawara sauya ranar jarabawar.




Post a Comment (0)
tsoffin labarai Sabbin Labarai