Rikici Tsakanin Sabin Dalibai Da ICT Unit Na Nuhu Bamali Polytechnic Akan Kudin Post UTME

 



Wata karamar matsala tana kan afukuwa tsakanin dalibai masu neman gurbin karatu a makarantar kimiya da fasaha ta Nuhu Bamalli Polytechnic zaria da ban garen da ke kula da shafin yanar gizo makarantar wato ICT unit.


Wanan matsala dai ta fara afkuwa ne tun ranar  7 ga watan decemba 2020, inda dalibai suka biya kudin post UTME a shafin makarantar, ama yaki nuna wa cewa sun biya domin karasa cike form din post Utme din su.


Jaridar my arewa school ta tunbe kamfanin Eschool dake kula da amsar kudin tare da ICT unit din Makarantar ama har yanzu ankasa samar da masalaha.


Company eschool yace kudin fah sun shiga asusun makarantar ama makaranta ne ke da alhakin gyra matsalar.


sukuma a bangaren ICT da muka tuntube su  sunce matsala ce ta bai daya  zasu gyara kafin kwana uku ama yanzu haka matsalar ta dauki mako 2 ba agyara ba.


Wanan bashi bane karon farko da aka samu matsalar shigan kudi yaki nunawa ga dalibai a makarantar, tun bayan sauya shafin makarantar aka fara samun wanan matsalar inda akasamu irrinsa a lokacin biyan kudin makarantar kakar 2019/2020.


Akarshe Muna kira ga :

1. Rijitrar Makarantar

 2. Deen Students Affair, 

 3. SUG President


Da su shiga cikin wanan al amari don samar wada daliban mafita, sanan akara wa'adin rufe rijista post utme  da dage ranar bada admission kamar yada hukumar ta fitar a jadawalin karatun ta, don daliban su samu sukara sa rijista domin dole sai sunyi rigista zasu iya samun gurbin karatu.

Post a Comment (0)
tsoffin labarai Sabbin Labarai